Sau da dama zababben shugaban kasar Amurka Donald Trump ya ambaci kafa “Zamanin zinari” a Amurka, tun bayan da ya sake darewa ragamar mulkin kasar, har ma ya ce shugaban kasar na 25 William Mckinley ya samar da manyan sauye-sauye ga Amurka bisa matakan haraji da ya dauka. To amma abun tambaya a nan shi ne shin matakin haraji da Trump ya dauka zai iya farfado da masana’antun kasarsa ko zai haifar da sabanin hakan—wato girbar abun da ya shuka.
A karni na 19, ko da yake dokar haraji ta Mckinley da ta Dingley sun taimakawa Amurka wajen sauya salonta daga kasa mai dogaro kan aikin gona zuwa kasa mafi karfi a bangaren masana’antu. Amma, illolli sun faru yayin da ake aiwatar da ita, daga cikinsu illa mafi tsanani ita ce hauhawar farashi. Alkaluma na nuna cewa, daga shekarar 1897 zuwa 1907, yawan kudaden da al’ummar kasar suka kashe a yau da kullum ya karu da kashi 33%. A sa’i daya kuma, buga karin harajin da Amurka ta yi ya haifar da gogayyar ciniki tsakanin kasa da kasa. Hakan ya sa, shahararren mai nazarin tarihin tattalin arziki na Amurka Douglas A. Irwin ya ce, matakin harajin da aka dauka a wannan zamanin da ake kira “Zamani mai feshin ruwan zinariya” ba ya haifar da tasiri mai amfani ko mummunar illa.
- Ofishin Siyasa Na Kwamitin Tsakiyar Jks Ya Kira Taron Nazarin Ayyukan Kiyaye Muhallin Halittu Da Sauransu
- Jakadan Kasar Sin Ya Bukaci Hadin Gwiwar Inganta Amfani Da AI Don Amfanar Da Kowa
Sai dai a wannan karnin da muke ciki na 21, yadda Trump ke kwaikwayon Mckinley da nufin kafa “Zamani na zinari”, zai habaka mummunan illolin da matakan haraji ke haifarwa, a maimakon farfado da masana’antun kasar.
Daukar matakan haraji ba za su kai ga warware matsalolin da ake fuskanta ta fannin sana’o’in samar da kayayyaki a cikin gidan kasar Amurka ba. Shafin yanar gizo na jaridar Financial Times ta Birtaniya ya ba da labari kwanan baya cewa, manufofi marasa tabbaci na gwamnatin Amurka, da ma rashin samun kudaden tallafawa, har da rashin kwadago da sauransu matsaloli ne da Amurka ke fuskanta, kuma sun hana bunkasar masana’antun kasar. Gwamnatin Trump na matukar son daidaita wadannan matsaloli bisa matakan haraji kadai, amma ba za ta cimma nasara ba ko kadan. A maimakon haka, Amurka na shan dacin wannan mataki——kafofin yada labarai kamar su CBS sun ba da labari cewa, a ran 25 ga watan nan da muke ciki kawancen manyan kamfanonin kasa da kasa na Amurka da aka san shi da sunan “Conference Board” ya gabatar da rahoton ma’aunin CCI da ta shaida kwarin gwiwar masu sayayya, wanda ya nuna cewa CCI na Amurka na kara raguwa a wannan wata. Ban da wannan kuma, masu nazarin tattalin arziki na Goldman Sachs sun rage hasashen da suka yi wa saurin bunkasuwar GDPn Amurka a karshen rubu’in shekarar 2025 daga 2.2% zuwa 1.7%. A sa’i daya kuma, kasashe da dama na daukar matakin haraji don mai da martani kan Amurka. Amurka tana mayar da kanta saniyar ware ke nan.
Kasancewar kasa da kasa na kara cude-ni-in-cude-ka a hada-hadar cinikayya da tsarin samar da kayayyaki, wanda hakan ke bukatar hadin gwiwar kasa da kasa, kuma Amurka na mai da kanta saniyar ware, ta kuma girbi abun da take shukawa, bisa matakan kariyar ciniki da ta dauka. (MINA)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp