Ofishin wakilcin Amurka a fannin cinikayya, ya fitar da wani rahoto a baya bayan nan mai taken “Rahoton 2023 game da yadda Sin ta sauke nauyin dake wuyan ta a kungiyar cinikayya ta duniya ko WTO”, wanda a cikin sa Amurka ta yi watsi da nasarorin da Sin ta cimma a fannin yin biyayya ga tsarin kungiyar, da sukar manufofi, da tsare tsaren tattalin arziki da cinikayya, wanda hakan a cewar Amurka ya haifar da babban kalubale ga hada-hadar cinikayya ta duniya.
To amma abun tambaya a nan shi ne wane mizani ne za a iya amfani da shi wajen auna biyayya ga manufofin kungiyar ta WTO? Amsa a nan ita ce, ba wani Amurka na da burin kare dokokin WTO ba ne, maimakon haka, fatan ta shi ne kafa nata ka’idojin da take burin kowa ya bi su.
- Shugaban Kasar Saliyo Zai Kawo Ziyara A Kasar Sin
- Wani Sojan Amurka Ya Bankawa Kansa Wuta Don Nuna Goyon Bayansa Ga Falasdinawa
Daga rahoton na Amurka, ana iya gane cewa, fatan Amurka shi ne Sin ta yi watsi da matakan biyayya ga kudurorin WTO, ta kuma sauya daga matsayin ta na nacewa salon tattalin arziki na gurguzu mai halayyar musamman na Sin, kana Amurka na son ganin Sin ta gudanar da sauye-sauye daidai da bukatun Amurka. Ko shakka babu rahoton na Amurka na da boyayyiyar manufa da ta sabawa abun da ya fara bayyanawa a farko.
Ko da an maimaita karya sama da sau dubu ba za ta sauya matsaya ba. Kuma duk yadda aka tsara rahoton Amurka, ba zai iya sauyawa daga matsayin sa na karairayi da farfagandar siyasa ba. (Mai fassara: Saminu Alhassan)