Gwamnatin tarayya ta ayyana ranakun Juma’a, 21 da Litinin 24 ga Afrilu, 2023 a matsayin ranakun hutu domin bikin karamar Sallar bana (EIdeil-Fitr).
Wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban sakataren ma’aikatar harkokin cikin gida, Shuaib Belgore, a ranar Laraba, ya bayyana cewa, minista Ogbeni Rauf Aregbesola ne ya bayyana hutun a madadin gwamnatin tarayya.
Aregbesola, ya taya daukacin al’ummar Musulmi murnar kammala azumin watan Ramadan, ya bukace su da su yi koyi da kyawawan dabi’u, soyayya, hakuri da juna, zaman lafiya, barin son zuciya, sadaukarwa kamar yadda Annabi Muhammad SAW ya yi umurni da shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp