Shafin dake zakulo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma, ciki sun hadar da; zamantakewa na rayuwar yau da kullum, Zaman Aure, rayuwar matasa, soyayya da dai sauransu.
Tsokacinmu na yau zai yi duba ne game da yadda karatun ‘ya’ya mata ke tafiya a yanzu, musamman ta yadda wasu matan ke korafi game da ci gaban karatunsu bayan aure, musamman yadda nauyi ke hawa kansu sabanin lokacin da suke gida.
Yayin da gefe guda kuma mafi yawan mutane ke korafin matsalolin da ake samu wajen ‘yan matan da suke karatu kafin aure.
Dalilin hakan ya sa wannan shafi ya ji ta bakin wasu daga cikin mabiyansa game da wannan batu; Ko wanne amfani ga ‘ya mace, tsakanin karatun boko kafin aure da kuma bayan aure?, Wanne irin matsaloli ne ke afkuwa ga kowanne bangare. Ta wacce hanya za a iya magance afkuwar hakan?.
    Ga dai ra’ayoyinnasu kamar haka:    Â
Sunana Zainab Zeey Iliysu, Jihar Kaduna:
Gaskiya a nawa tunanin karatu kafin aure ya fi akan bayan aure, duba da yadda mata ke shiga wasu sabgogin idan suka yi aure wajen kula da maigida da kuma wasu sabgogin musamman idan an samu yara, ba kamar mace idan tana gida ba, ba tada nauyin kowa kuma iyayenta za su yi mata uzuri sabida karatun da take yi, amma shi miji ba lallai yayi uzuri ba, sai an samu me fahimta sosai. Yin karatu bayan aure yana janyo rashin kula da karatun sabida rashin lokacin kai, yana kuma janyo matsaloli tsakanin mata da miji sai idan me fahimta ne, da dai sauransu.
Sunana Aminu Adamu, Malam Madori A Jihar Jigawa:
To magana ta gaskiya dukkaninsu sunada amfani tunda neman ilimi ne, to amma batun kafin aure ko bayan aure wannan yana faruwa ne idan har saurayin da budurwar suka zabarwa kansu hakan. To magana ta gaskiya kowanne yana da matsalolin sa, musamman karatu kafin aure domin a wasu lokutan wasu ‘yan matan tarbiyyar su tana lalacewa ta hanyar debo munanan dabi’u wanda raba su da ita yake zama wahala. To hanyar magance wannan matsala ita ce; iyaye su dage wajen bawa ‘ya’yansu tarbiyya ta addini da kuma kokari wajen dauke musu dukkanin wata dawainiya ta karatun da ma bukatun yau da kullum domin haka ne zai sa su kama kansu da kaucewa tarkon bata gari. To shawara ita ce; iyaye su dage wajen kula da tarbiyyar ‘ya’yansu akan tafarkin addinin musulunci domin haka ne zai taimaka su kula da kansu wajen tsare mutuncinsu, sai kuma iyaye su yi kokari wajen dauke nauyin karatun ‘ya’yansu da ma dawainiyar yau da kullum, sannan kuma iyaye su dage da addu’ar Allah ya shirya musu ‘ya’yansu, daga karshe su kuma ‘yan matan ya kamata su ji tsoron Allah su tsare mutuncin iyayensu da mazajensu.
Sunana Hafsat Sa’eed, Jihar Neja:
Ni a tawa fahimtar kayi karatu kafin aure ya fi muhimmanci sosai. Amfaninshi kuwa shi ne; koda karantarwa ne kana iya yi ka taimaki ‘ya’yanka don mazan hausawanmu yawancinsu ba sa duba ‘ya’ya ko karatunsu na abinci ma da ‘ya’ya suke bayarwa sai sun ga dama. Akwai matsaloli da yawa dake afkuwa ga rashin karatun ‘ya mace miji ya rasu ya barki da ‘ya’ya babu yadda za ki yi ki biya kudin karatunsu ko abinci wani ma gidan haya suke. Ni ina ganin hanyar magance shi, shi ne iyaye su bar ‘ya’ya su yi karatu don zai taimaki kansu. Shawarata ga ‘yan mata shi ne su yi karatu don su taimaki kansu da ‘ya’yansu a gaba don wasu matsalolin daga yaran ne ba sa son karatu. shawarata ga iyaye su bari ‘ya’ya su yi karatu kafin aure saboda bayan auren matsala ce.
Sunana Yahaya Adam Aliyu, Karamar Hukumar Dala, Jihar Kano:
To magana ta gaskiya ya fi kyautuwa mace tayi karatun boko a cikin gidan mijinta ya fi. Magana ta gaskiya da akwai matsaloli a kowanne bangare; Rashin samun kawaye nagari (classmates), Rashin kamun kai, matan aure wasu daga ciki suna amfani da damar su ta ganin sunada aure domin sabawa Allah. To ya kamata duk mutumin da matarsa take yin karatu to ya kamata na farko ya taya ta da addu’a, ya kula da duk matsalolinta ya sa Ido a harkokin makarantarta ya bata shawara akan ta ji tsoron Allah ta sani ita matar aure ce. Su kuma ‘yan mata iyaye aikin kune ku kula da tarbiyyar ‘ya’yanku gida da waje. Su kuma ‘yan mata su ji tsoron Allah su tuna cewa za su mutu kuma za su je lahira za a yi hisabi kuma kowa zai girbi abin da ya shuka.
Sunana Amina Ibrahim, Jihar Kaduna:
Ni a gani na karatun kafin aure ya fi ace mace ta fara bayan tayi aure, sabida mazan ba bari suke yi ba koda an yi alkawari da su, idan ta fara a gida koda ba ta kammala ba sai ta karasa a gidanta. Sai dai wani lokacin yin karatun da aure ya fi kafin aure, sabida matsalolin rayuwa da ake fuskanta na rashin kamun kan wasu matan, amma idan da auren dole ne mace ta kama kanta ko bata so. Shawarata ga kowanne bangare a ji tsoron Allah, a rinka tunawa da ubangiji, Allah ya sa mu gyara.
Sunana Ibrahim ismail, Jihar Kano:
Gaskiya gara a ce mace bayan tayi aure ya zamana ta dora da karatu, sabida irin kadami da mata suke fuskanta wurin rashin aure da wasu matan suna shiga ko kuma ana tilasta musu, amma aure yanada kariya wurin duk wanda ya san macen aure ce ke ba zai samu fuska wurin zuwar wa mace da harkar da bata dace ba, duk da wasu mazan suna ganin duk mahimmacin karatun da budurwa take da zarar mace tayi aure kawai ta hakura, amma ni a ra’ayina gara a ce bayan tayi aure ta ci gaba ya fi dacewa.
Sunana Lawan Isma’il (Lisary Rano) Karamar Hukumar Rano, Jihar Kano:
Maganar gaskiya a nawa ra’ayin karatun ‘ya mace kafin aure ya fi amfani duba da a lokacin shi ne take da lokaci isasshe kuma a wannan matakin ma sai ta fi samun karatun. Matsalar karatun ‘ya mace kafin aure ba zan iya cewa akwai ba, amma idan ta yi aure ne kuwa akwai, domin za ta ci karo da sa’ido daga wajen mijinta, iyayenta da sauran mutane domin za ta hadu da wasu mazan wadanda ba muharramanta ba. Sannan wasu matan za su fake da wannan damar ta ganinsu matan aure ne sai suna fasikanci da wasu mazan.Hanyar kawai ita ce idan da hali tayi karatunta tun kafin aure. Shawarata anan ita ce; su iyaye su daure su yi iyakar kokarinsu wajen ganin ‘ya’yansu sun yi karatun tun kafin su yi aure. Su kuma ‘yan mata su guji sawa a ransu cewa koda sun yi aure za su ci gaba da karatu indai ba ya zama dole ba domin idan har ki ka samu ki ka yi aurenki to ki bi Allah ki bi mijinki ki nemi sana’a kawai ba wai kina hangen aikin gwamnati ba, musamman idan baki sami damar yin karatun bokon ba tun a gidan iyaye ba.