Wakilin din-din-din na kasar Sin a MDD Fu Cong ya koka game da yadda batun Falasdinu ya zamowa duniya “kadangaren bakin tulu”, inda ya yi kashedin cewa, a kullum tashin hankali a Gaza na ci gaba da tsawaita, tare da hallaka karin fararen hula, a gabar da cikakken yaki ke neman barkewa a Gabas ta Tsakiya baki daya.
Tabbas rikicin Palasdinu da Isra’ila da aka shafe tsawon shekara guda yana gudana, ya zama wani muhimmin batu dake jan hankalin al’ummar duniya. Batun kare hakkin bil adama da na wanzar da zaman lafiya da kullum kasashen duniya ke furtawa, ya zama wani abu da yanzu ake amfani da shi a matsayin makami na siyasa da nuna fuska biyu da kuma haifar da wariya, maimakon ainihin ma’anarsa.
- Gwamnatin Zamfara Ta Mika Ta’aziyya Ga Iyalan Rundunar CPG Da ‘Yan Bindiga Suka Kashe A Jihar
- ‘Yan Bindiga Sun Sace Likitan Mata A Zamfara
Manyan kasashen duniya kan fake da batun ne idan suna da wani muradi da suke son cimmawa ko kuma neman shafa bakin fenti kan wasu kasashe. Yadda wasu kasashen ke mayar da hankali wajen kakkaba takunkumi ko yayata karairayi game da batun hakkin bil adama, abun takaici ne, la’akari da yadda suka yi biris ko ma suke kara rura wutar take hakkin mutane masu rauni a yankin Gabas ta Tsakiya.
Dukkanin bil adama na da hakkin da ya kamata a kare, haka kuma suna da ’yancin rayuwa. Daukar bangaranci a wannan rikici da kullum ke kara habaka, ba zai amfanawa duniya da komai ba sai karin rarrabuwar kawuna da tsana da rikici.
Kamata ya yi kasashen da suke ganin kansu manya ne, su karkatar da lokaci da karfi da ma albarkatun da suke zubawa wajen yada jita-jita da karairayi, wajen kai dauki ga masu rauni da kuma lalubo mafita mai dorewa ga wannan rikici da ya ki ci ya ki cinyewa.
Babu wanda zai tsira idan wani sashe na duniya na fama da rikici. Don haka, lokaci ya yi da ya kamata a daina nuna bangaranci, a hada hannu da kasashe masu kaunar zaman lafiya kamar Sin, dake kira da a shawo kan rikicin ta hanyar tattaunawa da lumana da samar da mafita da za ta karbu ga dukkan bangarori domin hankalin kowa ya kwanta.