A yau Talata ake kammala taron duniya kan Kirkirarriyar Basira ta AI, wato AI Action Summit a birnin Paris na kasar Faransa.
Batun kirkirarriyar basira ko AI, batu ne da duniya ke mayar da hankali kai matuka, kasancewarsa wani sabon abu da ya zo da gagarumin sauyi a bangaren fasahohi na zamani. Wani misalin samfurin AI na baya-bayan na da ya dauki hankalin jama’ar duniya, shi ne fasahar AI ta R1 ta kamfanin Deepseek na kasar Sin. Zan iya cewa wannan sabon samfuri ya ja hankali ne saboda yadda ya zo da matukar ingancin da zai yi takara kafada da kafada da takwarorinsa na kasa da kasa kamar ChatGPT, wanda aka samar da shi ba tare da kashe kudi mai yawan na takwarorinsa ba, duk kuwa da irin kalubalen da ya fuskanta kamar shingen Amurka na samar da na’urar Chip ga kamfanonin Sin.
- Gwamna Nasir Ya Sauke Sakatarorin Hukumar Ilimi Na Kananan Hukumomi 21 A Kebbi
- Sin Za Ta Ci Gaba Da Tallafa Wa Kokarin Afirka Na Samar Da Wutar Lantarki Mai Tsabta
Abun takaici shi ne, maimakon rungumar wannan fasaha da daukar darasi da dabaru daga gare ta, kamar kullum, masu neman dakile kasar Sin ta kowace fuska na neman shafa mata bakin fenti da fakewa da batun kare sirri ko tsaron kasa.
Bisa la’akari da basira da kwarewar da fasahar AI ke tattare da su, kamata ya yi duniya ta hada hannu domin ganin an samar da tsari guda na tafiyar da harkokin da suka shafeta, ta yadda za ta amfani al’umma kamar yadda ake fata. A daidai lokacin da ake bukatar hadin gwiwa da hada karfi da karfe domin samun ci gaba, wasu kuwa babu abun da suke bukata face kawo rarrabuwar kawuna da kokarin mayar da wata kasa saniyar ware.
Da yake jawabi game da wannan batu a jiya, mai masaukin baki, shugaban Faransa Emmanuel Macron, ya ce, “ba na tunanin ya dace a haramta amfani da wata fasaha saboda kasar da ta fito” yana mai cewa Faransa “ba ta bin tsarin Amurka” na amfani da fasahohi saboda asalinsu. Wadannan kalamai sun nuna cewa, bai kyautu a rika sanyawa wata fasaha karan tsana saboda asalinta ba, don kai ana ganin inda ta fito din, ya samu gagarumin ci gaba.
Har kullum, na kan ce, ci gaban kasar Sin wata dama ce ba kalubale ba. A matsayin ’yar Afrika, ci gaban kasar Sin daidai yake da ci gaban nahiyar Afrika domin duk wata nasara da ta samu, ba ta kyashin kai wa Afrika, kuma burinta shi ne ta ga nahiyar ta amfana, ta samu ci gaba, kuma al’umma sun kasance cikin walwala. Kamata ya yi wannan ra’ayi na kasar Sin na neman ganin ci gaban kowa, ya kasance ra’ayin kasashe manya masu son ganin ci gaban duniya, sai dai yayin da ake fafatukar ganin haka, manyan kasashen su ne ke kokarin dankwafe duniya daga samun irin ci gaban da al’umma ke muradi. (Faeza Mustapha)