A karon farko, karfin lantarkin da tashoshin samar da lantarki da ba sa amfani da man fetur da kwal da Sin ta kafa suka samar, ya zarce kilowatt biliyan 2 zuwa karshen watan Fabrairu.
Wannan na kunshe ne cikin sabon rahoton da majalisar kula da lantarki ta kasar Sin ta fitar, wanda ya ce adadin shi ya dauki kaso 58.8 na baki dayan lantarkin da tashoshin samar da lantarki na kasar Sin ke samarwa.
Karfin lantarki da tashoshin samar da lantarki daga sabon makamashi da suka hada da iska da na hasken rana ke samarwa, ya kai kilowatt biliyan 1.46 zuwa karshen watan da ya gabata, adadin da ya dauki kaso 42.8 na jimilar lantarkin da kasar ke samarwa. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp