Bisa matakan rura yakin cinikayya, ta yadda za ta kai ga kakabawa juna haraji, kasar Amurka ta tarwatsa kyakkyawan tsarin cinikayya na duniya wanda aka gina bisa cin gajiyar ingancin hajoji da hidimomi, da kwarewar samar da su, da cimma moriyar juna, ta kuma dauko hanyar illata tattalin arzikin kanta da na sauran sassan kasa da kasa.
Sanin kowa ne cewa, a yanzu haka shugaban Amurka Donald Trump ya riga ya sanya hannu kan dokar shugaban kasa, wadda ta tanadi kakaba karin mafi karancin harajin fiton kayayyaki har kaso 10 bisa dari, kan hajojin da ake shigarwa kasar, da karin kason da zai haura 10 bisa dari kan kayayyakin wasu abokan cinikayyar kasar ta Amurka, kamar dai yadda ya alkawarta tun a baya.
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Kwamandan ‘Yan Sa-kai, Sun Jikkata Wasu A Katsina
- Mun Rage Tasirin ‘Yan Bindiga A Kebbi Da Zamfara – Sojoji
Bisa wannan mataki, ma iya cewa gwamnatin Trump ta kara nunawa duniya cewa manufofinta na cinikayya an gina su ne bisa tushe marar nagarta. Ko da yake wani na iya cewa wannan mataki na “Dora min haraji ni ma na dora maka”, ya yi kama da adalci, amma fa a tsarin tattalin arziki hakan babban kuskure ne. Sabanin haka, baiwa kasashe daban daban damar cin gajiyar fifikonsu a wasu sassa, shi ne abun da zai baiwa kowa damar cin gajiya daga fannonin da yake da karfi, kana sauran sassa ma su samu ta su gajiyar daga wasu fannonin.
Ga misali, Amurka na shigar da akasarin gahawar da take amfani da ita ne daga ketare, don haka take dora harajin fito dan kadan kan gahawar dake shiga kasar. Amma da yake kasar Brazil ce kan gaba a duniya wajen fitar da gahawa, ta dora harajin kaso 9 bisa dari kan gahawar da za a rika shigarwa kasar daga ketare. Ke nan da a ce Amurka ita ma za ta dora harajin gahawa daidai da na Brazil, abun da hakan zai haifar shi ne karuwar farashinta a cikin Amurka da kuma durkushewar sashen sarrafa ta a cikin kasar. To, haka abun yake a kusan dukkanin hajojin da ake shigarwa ko fitarwa daga kasashe daban daban.
Masana da masharhanta daga sassan duniya daban daban dai na ta bayyana suka kan matakin gwamnatin Trump na kara wannan haraji, inda akasari ke cewa hakan zai haifar da karin gibin cinikayya ne ga kasar ta Amurka. Inda wasu ke cewa hakan zai rage ingancin tattalin arzikin kasar da kusan kaso 3 bisa dari, tare da illata sassan kasuwancin kasar baki daya. Don haka dai muna iya cewa da wannan karin haraji, Amurka “Ta debo ruwan dafa kanta”! (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp