Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana a yau Alhamis cewa, tun daga karo na farko, bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin wato CIIE ya samar da sauki ga kasashe mafi karancin ci gaba don halartar bikin. A cikin shekaru 7 da suka gabata, karin kayayyaki daga kasashe mafi karancin ci gaba sun shiga kasuwar kasar Sin ta bikin CIIE, hakan ta sa kaimi ga kasashen da su bunkasa sana’o’i da kyautata zaman rayuwar jama’arsu baki daya.
A gun bikin CIIE a wannan karo, kasashe mafi karancin ci gaba guda 37 sun halarci bikin, sashen karbar bakuncin gudanar da bikin ya samar da shaguna fiye da 120 ga kamfanonin kasashen kyauta. Kana an fadada fadin shagunan kayayyakin Afirka a reshen abinci da amfanin gona don nunawa masu halartar bikin kayayyaki masu salon Afirka.
Hakazalika, Mao Ning ta bayyana a gun taron manema labaru cewa, Sin tana maraba da zartas da kudurin da Sin ta gabatar na sa kaimi ga yin hadin gwiwar kasa da kasa a fannin kiyaye tsaron duniya a gun kwamitin kula da kwance damara da kiyaye tsaron duniya na babban taron MDD karo na 79. Mao Ning ta kara da cewa, Sin ta riga ta mai da aikin aiwatar da kudurin a matsayin muhimmin aikin hadin gwiwa kan kiran kiyaye tsaron duniya, tana son yi kokari tare da bangarori daban daban wajen sa kaimi ga aiwatar da kudurin a dukkan fannoni yadda ya kamata, ta hakan za a sa kaimi ga amfanawa sha’anin kiyaye zaman lafiya da samun bunkasuwa na dan Adam ta hanyar raya kimiyya da fasaha. (Zainab Zhang)