Kamfanoni masu yawa musamman ma matsakaita da kanana za su rufe su bar Nijeriya zuwa wata kasa, saboda matsalolin da suke fuskanta wajen tafiyar da harkokinsu, wannan kuwa ya biyo bayan sanarwar kamfanonin raba wutar lantarki ta kara farashin kudin wutar lantarki daga ranar 1 ga watan Yuli 2023.
Idan za a iya tunawa, a shekaru takwas kadai da suka gabata lokacin da kamfanoni fiye da 50 da suka hada da Dunlop da Michelin wadanda suke yin tayoyi suka koma wata kasa, inda suke aikowa da tayoyin da suka yi a sayar a Nijeriya sakamakon karanci da kuma tsadar wutar lantarki.
Abin lura a nan shi ne, akwai ma’aikata da yawa wadanda suka rasa ayyukansu sanadiyar irn wannan al’amari hakan.
Jaridar LEADERSHIP ta yi bincike da ya nuna cewa za a kara kudin wutar lantarki a daukacin Nijeriya saboda kamfanonin raba wutar lantarki 11 (DisCos) za su fara amfani da aiwatar da sabon tsarin biyan farashin a wata mai kamawa.
Tuni dai kamfanin raba wutar lantarki na Abuja AEDC ya ba da sanarwar, kudin wutar lantarki daga 1 ga watan Yuli 2023.
Idan aka yi la’akari da sanarwar da kamfanin ya yi, karin kudin wutar lantarkin zai fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Yuli, saboda yadda al’amarin canjin kudaden kasar waje zuwa naira abin ya dauki wani sabon salo mai daure kai.
Sanarwar ta nuna cewa, “1 ga watan Yuli 2023 akwai karin kudin wutar lantarki, hakan ta kasance ne saboda yadda al’amarin canza kudi musamman tsakanin naira da dala ya dauki sabon salo.
“A karkashin tsarin MYTO 2022, wanda a shekarun baya maganar ana canza kudin ne a kan dala daya da ake sayarwa kan naira 441, amma a yanzu abin ya koma dala 1 ana sayar da ita fiye da naira 750, wanda ba karamin tasiri abin zai yi ba a kan al’amarin samar da wutar lantarki kamar yadda sanarwar ta bayyana”.
Masu amfani da wutar lantarki da suke tsakanin nau’in B da B da kuma C, suna amfani da wutar lantarki awa 12 zuwa 16, sabon farashin nasu kan naira 100 ko wace kilowatt, yayin da su kuma masu nau’in A (masu awa 20 da fiye da haka) da nau’in B (awa 16 zuwa 20) wadanda za su biya kudi masu yawa.
“Ga wadanda suka riga suka biya kudaden da suka kamata a biya ana iya samun kari, amma bai taka kara ya karya ba a takardar bayanin wutar da aka yi amfani da ita da kudin da suka kamata a biya na karin sai dai wannan zai fara ne a watan Agustan 2023 kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Haka nan duk dai irin sakon daga kamfanin raba wuta na Ikeja shi ma ya fitar dangane da karin kudin wutar lantarki, ya sanar da al’umma da ke hulda da kamfanin cewa zai kara kudin wutar daga ranar 1 ga watan Yuli, inda shi ma yake ba da dalilan da sauran kamfanonin suka bayar.
Da yake bayyana nasa ra’ayin kan karin kudin wutar lantarki da za a yi, shugaban kungiyar masu masana’antu ta kasa ya yi magana da kakkausar murya, inda ya ce yawancin kamfanoni musamman matsakaita da kananan za a tilasta masu barin Nijeriya, saboda irin halin da suke fuskanta kan yadda suke tafiyar da harkokin kamfanoninsu cikin yanayi na tsadar kayayyaki wadanda ba su lissafuwa.
Da yake ba da misali da karin kudin farashin man fetur bayan da aka cire tallafi wanda hakan ne ya sa suke fuskantar matsala wajen sayo injunan da suke amfani da su, wannan bayan samun karuwar kashi 40 na karin kudaden yadda za su rika sa wa janareta da suke amfani da su wajen gudanar da ayyukansu.
Maganar da ake ta Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu zai jawo hankalin masu zuba jari su zo Nijeriya abin na iya zama wata tatsuniya idan aka yi la’akari da irin cikin mawuyacin hali na tafiyar da harkokin kamfanoni a Nijeriya suka kasance a yanzu.
A nasa tsokacin, shugaban kungiyar manyan ma’aikata na kayan marmari da taba ta Nijeriya (FOBTOB), Komrade Jimoh Oyibo, ya ce bangaren da ya kan samar da ayyuka da suka kai fiye da miliyan daya da rabi 1.5 ya rasa ayyuka fiye da 1,478, bayan hakka kamfanoni fiye da goma suka rufe saboda da irin halin da ake fuskanta na matsalar da ta shafi canjin dala, wannan yana nufin yawancin kamfanoni da suka hada da matsakaita da kanana tamkar an tilasta masu ne na rufe harkokinsu sanadiyar hakan.
Binciken da jaridar LEADERSHIP ta yi ya bayyana miliyoyin ma’aikata za su rasa ayyukan yi saboda tsauwalar farashin kaya na harkokin kamfanoni, wadanda zai yi masu matukar wuya su ci gaba da harkokinsu, hakan zai sa ko dai su rufe su kuma su koma wasu kasashe. Alal misali kananan kamfanonin ruwa sun fara tunanin irin matakin da za su dauka dangane da hakan.
Sun ce karin kudin mai da bai wuce mako uku ba bayan da kudin sufuri ya karu sai aka samu karin kudin kayan abinci da sauran wasu kayan, wannan an danganta hakan ne a kan cire tallafin mai, wanda hakan ne zai kara jefa ‘yan Nijeriya cikin fatara.
Shi kuma, Dakta Innocent Ihennacho Ogbonna ya bayyana shirin karin kudin wutar lantarki da aka yi na nuna gwamnati ba ta damu da halin da al’ummarta suke ciki ba. Ya ce tuni aka tura su bango idan aka yi la’akari da irin kuncin rayuwar da ake fuskanta a Nijeriya.
Kamar dai yadda ya ci gaba da yin bayani, Ogbonna ya kara jaddada cewa,”Tuni kamfanoni da yawa suka fara fuskantar wahala, musamman ma yadda za su samu injunan da za su samar masu da wutar lantarki da za su yi amfani da ita.
Amma ganin yadda aka samu karin kudin wutar lantarki wannan ya nuna sauran ‘yan Nijeruya sai su koma yin amfani da ita ce da kuma fitila, hakan ma kamfanoni ko masana’antu za su fuskanci babbar matsala da ci gaba da harkokinsu na tsadar rayuwa ta kayan aiki da karin wutar lantarki, daga karshe su rufe kamfanonin.
“Karin kudin wutar lantarki wani abu ne da ke nuna ba a damu da halin da ‘yan Nijeriya suke ciki ba, saboda shi talaka babu inda zai je a saurari kukansa, yayin da su kotunan da ake masu kallon can ne talaka zai je a bi masa hakki, yanzu al’amarin siyasa ya yi masu katutu”
Shugaban kungiyar muhalli na Nijeriya, Komrade Onwumere John ya bayyana shirin karin wutar lantarki zai sa wasu harkokin kasuwanci su tsaya, ma’aikata kuma su kara shiga halin ni ‘yasu.
Onwumere ya ce, “Wannan a zahiri ya nuna shugabanni ba su damu kowane irin hali talaka ya shiga ba babu ruwansu. Ya kamata su gane cewa talakawa yanzu ba su dafa abinci saboda ba su iya sayen kananzir. Shugaban kasa Tinubu ya taimaka da tsare-tsare da za su taimaka wa talakawan Nijeriya abin da ya dace kenan ba a kame baki a yi shiru ba.
Shi ma a nashi jawabin, babban jami’i kuma shugaba na kungiyar masu masana’antu ta kasa, Mista Segun Ajayi-Kadir ya bayyana mambobinsu da cewa suna ta kokarin yadda za su ci gaba da harkokinsu, amma duk da hakan za a tilastama wasu daga cikinsu ko dai su rufe kamfanonin ko kuma su koma kasar waje.
Ya ce mabobin kungiyar sun kashe fiye da naira biliyan 144.5 wajen samar da yadda kamfanonin za suka tafiyar da aikinsu a shekarar 2022.
Ya ce, “Kamar yadda kungiyarmu ta bayyana masu masana’antu sun kashe akalla naira biliyan 144.5 wajen samar da yadda injinan da suka aiki da su a 2022, abin ya karu daga naira biliyan 77.22 a shekarar 2021.
“Wannan shi ya kai na kashi 87 na karin abin da za su yi amfani da shi wajen tafiyar da ayyukansu na kamfanoni kamar yadda su masu masana’antun suka bayyana a cikin shekarar, an kara kudin wutar lantarki da kashi 186.
Wata majiya mai tushe a banagaren da ya shafi wutar lantarki ta bayyana cewa karin kudin wutar lantarki yana iya kasancewa ba daya ba, wannan kuma idan aka yi la’akari da yawan kudaden da DisCos suka zuba shi zai nuna ga irin karin kudin da za a yi.