Hukumar hadin gwiwar ci gaba na kasa da kasa ta kasar Sin, wato CIDCA a takaice da hukumar ci gaban masana’antu ta MDD, da kuma ma’aikatar masanan’antu ta kasar Habasha, sun sa hannu kan sanarwar hadin gwiwa da ta shafi bangarorin uku ta yanar gizo jiya Litinin.
An ruwaito cewa, wannan ne karo na farko da hukumar hadin gwiwar ci gaba na kasa da kasa ta kasar Sin, wato CIDCA ta sa hannu kan takardar hadin gwiwa da ta shafi bangarori uku tare da hukumar MDD da wata kasar Afirka, inda suke aiki tukuru wajen kara inganta hadin gwiwa, da kuma inganta gudanar da ajandar ci gaban duniya tare.
- Ya Kamata Kasashen Yamma Su Ji Shawarwarin Kasar Sin Maimakon “Damuwa Da Asara”
- Bikin Bazara Na Shekarar Dabbar Loong Ya Baiwa Duniya Damar Ganin Muhimmancin Tattalin Arzikin Sin
Kakakin hukumar hadin gwiwar ci gaba na kasa da kasa ta kasar Sin, Li Ming ya bayyana cewa, hukumar ci gaban masana’antu ta MDD da hukumar da abin ya shafa na Habasha dukkansu abokan hadin gwiwar ci gaban kasa da kasa na bangaren Sin ne masu muhimmanci. Daga bisani, hukumar hadin gwiwar ci gaba na kasa da kasa ta kasar Sin za ta yi aiki tare da hukumar ci gaban masana’antu ta MDD da hukumar Habasha wajen inganta gudanar da ajandar ci gaban duniya, karfafa mu’ammala tsakaninsu, da sabunta hanyoyin tattara kudade, ta yadda sakamakon hadin gwiwa masu tarin amfani za su kawo alheri ga kasashe masu tasowa da kuma al’ummunsu.
Sanarwar da ta shafi bangarorin uku da suka sa hannu a wannan karo ta tabbatar cewa, za a kafa cibiya da za ta zama abin koyi a fanonnin aikin noma da aikin kiwon dabobbi da sana’ar sarrafa amfanin gona da samun ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba da sauransu. Za a samar da hidimomin ba da amsa kan manufofi da kuma tsarin ci gaba ga dukkan kasashen Afirka, ban da wannan, za a gudanar da hadin gwiwa daban daban kan fasahohi da horar da ma’aikata da sauransu. (Safiyah Ma)