“Kasar Sin na kafa ‘tarkon bashi’ a Afirka, tana kafa ‘sabon salon mulkin mallaka’……” A cikin ’yan shekarun baya bayan nan, kafofin yada labarai na kasashen yamma sun sha yayata irin wadannan karairayi, a kokarin lalata huldar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka da ma hadin gwiwarsu.
Kaza lika a kwanakin baya, irin wadannan kafofi sun kara fitar da wani tsokacin, inda jaridar “The Times” ta Burtaniya, a wani rahotonta mai taken “Sinawa na ba ’yan tawayen Najeriya rashawa, don neman mallakar albarkatun ma’adinai”, ta zargi kasar Sin da “samar da kudin tallafi ga harkokin ta’addanci a Najeriya.”
- Richard Sears: Harufan Sinanci Ba Kawai Na Kasar Sin Ba Ne, Al’ada Ce Mai Daraja Ga Duniya Baki Daya
Rahoton dai ya yi matukar jawo hankalin al’ummar Najeriya, har ma wasu da suke shan wahalar ta’addanci, da ma hare-haren ’yan tawaye sun fara nuna shakku ga hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka. A game da hakan, Ambassada Isma’il Ahmed, mai sharhi kan harkokin diplomasiyya a Najeriya, a yayin tattaunawa da mu ya yi nuni da cewa, “ba wai wani abun mamaki ba ne don sun yi amfani da kafafen yada labaransu, ko jaridu wajen sukar China, ai sun sha yi.”
Ambassada Isma’il Ahmed ya ce, “A cikinsu guda hudu kamar Sudan, Aljeriya, Najeriya da Masar, dukkanninsu za ka ga suna da man fetur, kuma China na sayen fetur daga wajensu, don haka dole Turawa su ta da hankalinsu, kuma har gobe tagomashi ake samu ta fuskar cinikayya da tattalin arziki. Duk kamfanonin da suke Najeriya yanzu, suke ayyukan gine-ginen hanyoyin mota, da na layin dogon jiragen kasa, da tasoshin jiragen sama, dukkan kamfanoni ne na China, saboda sun fi sauki, sun fi dadin alaka, sun fi amana, sun fi gudanar da komai ba tare da an sa siyasa a ciki ba. Saboda haka zai yi wahala nan gaba a ce wai Turawa za su samu hanyoyin da ake tunanin za su yi amfani da su, domin fitar da kasar China daga hulda da kasashen Afrika.
Yawanci su kasashen Turawa suna amfani da damar su ce wajen daurewa masu mulkin kama-karya gindi, su yi ta mulkin mallaka a kasashen Afirka, amma ka kula abubuwa suna ja baya a yanzu, masu mulkin mallakar su kan kare, kuma su kansu su kan karkata su koma bangaren China.”
To kamar dai yadda Ambassada Isma’il Ahmed ya fada, kasashen Afirka a matsayinsu na kasashe masu mulkin kai, suna da kwarewa wajen yanke shawara, kan ko hadin gwiwarsu da wata kasa na da amfani ko illa, kuma suna da ’yancin zabar abokan hadin gwiwa, kuma in an yi nazari, a cikin ’yan shekarun baya, hadin gwiwar cin moriyar juna a tsakanin Sin da kasashen Afirka ya samar da kyawawan sakamako na a zo a gani.
A karshe wannan rahoto na “The Times”, ya ce, “Najeriya kamar za ta ci gaba da zabar kasar Sin ta fannin zuba mata jari a maimakon kasashen yamma. Bayan ziyarar da mataimakiyar shugaban kasar Amurka Kamala Harris ta kai Afirka a wannan wata, mataimakin shugaban Nijeriya Yemi Osinbajo, ya yaba da alfanun da aka samu bisa ga tallafin da kasar Sin ta samar, kuma shi ma zababben shugaban Najeriya mai jiran gado Bola Ahmed Tinubu, tuni ya zanta da jakadan kasar Sin.”
A hakika, kullum kasar Sin tana maraba da sassan kasa da kasa, da su aiwatar da hadin gwiwa da kasashen Afirka, kuma sau tari ta sha bayyana cewa, Afirka dandali ne na hadin gwiwar kasashen duniya, a maimakon fagen takarar manyan kasashe.
Karya dai fure take ba ta ’ya’ya, wadanda suke makircin lalata hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka, muna ba su shawarar mai da hankalinsu a kan taimakawa kasashen Afirka, wajen tabbatar da ci gabansu a maimakon su rika yayata karairayi. Kasar Sin na maraba da karin kasashe su sa hannu a ayyukan raya Afirka, amma kuma tana adawa da niyya, da matakai na shafawa hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka bakin fenti. Baya ga haka, muna kuma jan hankalin abokanmu na Nijeriya, da kada su fada cikin tarkon da kasashen yamma suka dana na dakile bunkasuwarsu. (Mai Zane: Mustapha Bulama)