Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu da Mataimakinsa, Kashim Shettima da kuma sauran mukarrabansu da ke fadar gwamnatin tarayya, za su lakume kimanin naira biliyan 15.961 a harkokin tafiye-tafiyen cikin gida da kuma kasashen waje a 2024.
Adadin kudaden dai, na kunshe ne a cikin kudurin kasafin kudi na shekarar 2024, wanda a yanzu haka yana gaban majalisar dokokin kasar nan suna yin nazari a kai.
- Majalisar Dokokin Nasarawa Ta Amince Da Kasafin N199.9bn Da Gwamna Sule Ya Gabatar
- SERAP Ta Nemi Majalisa Ta Yi Watsi Da Bukatar Gina Wa Shettima Gidan Naira Biliyan 15
Adadin kudaden sun nuna cewa, Shugaba Tinubu zai lakume makudan kudade har naira biliyan 7.630 wajen tafiye-tafiye, inda mafi yawan kudaden za a kashe su ne wajen yin tafiye-tafiye a kasashen ketare.
Idan har majalisar kasa ta amince da kundin kudurin, zai lakume naira biliyan 6.992, wajen tafiye-tafiye a kasashen waje, yayin da zai kashe naira miliyan 638.535 na tafiye-tafiyen a cikin gida Nijeriya.
Haka zalika, shi ma Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima; zai kashe jimillar naira biliyan 1.847 a balaguron kasashen waje da na cikin gida.
A tsarin kasafin kudin, zai kashe naira biliyan 1.229 wajen tafiye-tafiye zuwa kasashen waje da kuma naira miliyan 618.399 a tafiye-tafiyen cikin gida Nijeriya.
Sannan, an kuma samar da naira biliyan 6.484 na ma’aikatan fadar shugaban kasa na tafiye-tafiye zuwa kasashen waje da cikin gida.
Wanda za su lakume naira biliyan 6.282 na tafiye-tafiyen zuwa kasashen waje, yayin da za su kashe naira miliyan 60.981 don horarwa da kuma naira miliyan 140.640 don tafiye-tafiyen cikin gida.