Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana kasafin kuɗi na 2025 a matsayin wata muhimmiyar taswira ta ƙarfafa tattalin arziki, daidaito na zamantakewa, da cigaban ƙasa.
Da yake jawabi a Taron Manema Labarai na Ministoci karo na uku na shekarar 2025 a Cibiyar Yaɗa Labarai ta Ƙasa da ke Abuja a ranar Talata, Idris ya ce wannan kasafin ya mai da hankali ne kan saka hannun jari a muhimman sassa da ke da tasiri kai-tsaye kan jin daɗin ‘yan Nijeriya da cigaban tattalin arzikin su.
- Majalisar Bayar Da Shawarwari Kan Harkokin Siyasa Ta Kasar Sin Ta Fara Taronta Na Shekara-shekara
- Kotu Ta Ɗaure ‘Yan Tiktok 2 Kan Yaɗa Kalaman Batsa A Kano
Ya ce: “Kasafin kuɗi na 2025 ba kawai takardar kuɗi ba ce; taswira ce ta inganta tattalin arziki, daidaito na zamantakewa, da cigaba mai ɗorewa.
“Wannan kasafin kuɗin ya nuna sabon gagarumin fifiko a kan harkar tsaro, ababen more rayuwa, ilimi, kiwon lafiya, ma’adanai, noma, da sauran sassa masu matuƙar tasiri kan jin daɗin al’umma da cigaban tattalin arzikin su.”
Ya ƙara da cewa shekarar 2025 ita ce “shekarar tabbatar da cigaba,” inda sauye-sauyen da gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta fara aiwatarwa za su fara haifar da ainihin sauyi ga al’umma.
Ya kuma jaddada cewa tun tuni aka fara ganin sauƙin farashin kayan abinci, wanda ke samar da sauƙin rayuwa ga ‘yan ƙasa.
Ministan ya tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da aiwatar da kasafin kuɗi yadda ya kamata domin tabbatar da ingantaccen tasirin sa a rayuwar ‘yan Nijeriya.
Ya ce, “Ina tabbatar wa da ‘yan Nijeriya cewa Gwamnatin Tarayya za ta yi aiki tuƙuru don ganin an aiwatar da kasafin kuɗi cikin tsari domin ya haifar da gagarumin tasiri a rayuwar al’umma. Saboda haka, ina kira ga ‘yan Nijeriya da su mara wa wannan ƙoƙari baya domin gina ƙasa mai cigaba da haɗin kai.”
Haka nan, Idris ya jinjina wa ‘yan jarida kan rawar da suke takawa wajen bayar da rahotanni na gaskiya da suka shafi cigaban ƙasa.
Ya buƙace su da su ci gaba da gudanar da aikin jarida bisa ƙa’idojin da suka dace domin ƙarfafa dimokiraɗiyya da inganta sanin makamar gwamnati a tsakanin al’umma.
“A wannan zamani da ƙarya ke yawaita wajen ruɗar da jama’a, jajircewar ku kan gaskiya da adalci ta fi zama dole fiye da kowane lokaci. Dole ne mu haɗa kai domin tabbatar da cewa labaran da ke tsara yadda ake tattauna batutuwan jama’a sun kasance bisa haƙiƙanin gaskiya, ba tare da son zuciya ko ƙazafi ba,” in ji shi.
Taron ya samu halartar Ministar Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari, Dr. Jumoke Oduwole, da Ƙaramin Ministan ma’aikatar, Sanata John Owan Enoh, da wasu jigajigan gwamnati.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp