Cibiyar binciken duniyar wata, karkashin hukumar kula da zirga-zirgar kumbuna a sararin samaniya ta kasar Sin, ta sanar da cewa, zuwa karo na 9, kasar Sin ta samar da kasar duniyar wata da jimilar nauyinta ya kai gram 125.42, ga kwararru masu nazarin kimiyya da fasaha na kasashe daban daban, ciki har da kason kasar duniyar wata da aka raba ma wasu hukumomin bincike 7 na kasashe 6. Kana bisa gudanar da bincike kan kasar da na’urorin binciken duniyar wata na kasar Sin, wato Chang’e-5, da Chang’e-6, suka dawo da ita, masu nazarin kimiyya da fasaha na kasar Sin da na sauran kasashe, sun gabatar da sakamakon bincike fiye da 150.
An ce, tsarin da ake bi wajen neman samun kasar duniyar wata, shi ne a mika bukatar samun kasar ta wani shafin yanar gizo mai alaka da ayyukan binciken duniyar wata da sararin samaniya na kasar Sin. Daga baya wasu kwararru na kasar Sin za su tantance bukatar da aka mika, gami da yanke shawara kan ko za a ba da kasar ko a’a.
Ban da haka, bayanan da hukumar kula da zirga-zirgar kumbuna a sararin samaniya ta kasar Sin ta samar, sun nuna yadda masu nazarin kimiyya da fasaha na kasar Sin ke karkata hankalinsu daga binciken labarin kasa na duniyar wata, zuwa na fasahar amfani da albarkatun duniyar wata, da samar da tubali don share fagen aikin gini a duniyar. A cewar wani jami’in hukumar kula da zirga-zirgar kumbuna a sararin samaniya ta Sin, an yi hakan ne don shirya fasahohin da ake bukata wajen gudanar da ayyukan kai mutane duniyar wata, da gina tashar bincike kan duniyar wata, a nan gaba. (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp