Bayan da Mr. Donald Trump ya sake hawan kujerar shugaban kasar Amurka, ya dakatar da kusan dukkan gudummawar da kasarsa ke samarwa ga kasashen ketare, bisa manufarsa ta wai “Amurka ta zamanto gaba da komai”. Sai dai a kwanakin baya, gwamnatin kasar Philippines ta sanar da cewa, Amurka ba ta dakatar da gudummawar soja ta kimanin dala miliyan 336 a gare ta ba.
To, amma me Amurka take iya samu daga gudummawar soja da take samarwa Philippines har ya sa ba ta dakatar ba? Dalili shi ne gudummawar na iya sa sojoji da ‘yan sanda da ma ‘yan siyasa na kasar ta Phillipines su taimaka mata cimma manufarta, musamman ma wajen neman dakile kasar Sin bisa ga yadda suke sa-in-sa a batun tekun kudancin kasar Sin.
Sai dai kuma, a yayin da hakan ke biyan bukatun wasu ’yan siyasar Amurka, a sa’i daya kuma yana lalata moriyar kasar Phillipines.
Kasar Philippines na mai da kanta saniyar ware, musamman sabo da yadda sauran kasashen shiyyar ke neman tabbatar da zaman lafiya da ci gaba na yankin, kuma ita za ta dandana kudarta game da gudummawar soja da Amurka ta ba ta. Kuma sam hakan ba zai gurbata yanayin zaman lafiya na yankin tekun kudancin kasar Sin ba. (Lubabatu Lei)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp