ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, November 12, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kasar Sin Ce Babbar Misali Na Yadda Ya Kamata Demokradiyya Ta Kasance

by CMG Hausa
3 years ago
Kasar Sin

Demokradiyya ita ce tsarin shugabanci dake mayar da hankali kan muradun al’umma. Wato dai, al’umma ne ya kamata su kasance kashin bayan demokradiyya.

Kuma kasar Sin ce babbar misali na yadda ya kamata demokradiyya ta kasance, domin a ganina, tabbatuwar tsarin demokradiyya ita ce, kasancewar al’umma cikin walwala da wadata da kwanciyar hankali.

  • Takardun Kudin Da Suka Shaida Yadda Kasashen Duniya Suka Ci Gajiyar Ci Gaban Kasar Sin

Yayin da yake kaddamar da babban taron wakilan Jam’iyyar Kwaminis ta Kasar Sin karo na 20 a Lahadin da ya gabata, shugaban kasar Xi Jinping, ya jaddada cewa kasar za ta kara inganta tsarin demokradiyyar dake mayar da hankali kan jama’a, wato jama’a ne za su kasance masu ruwa da tsaki a dukkan tsarukan demokradiyya a dukkan matakai.

ADVERTISEMENT

Abun da na fahimta shi ne, a ko da yaushe, JKS ta kan tsara manufofi da dabarun da za su tabbatar da cewa, al’umma ne ke kan gaba a duk wani abun da ya shafi kasar, wanda ke nuna yadda take mayar da hankali wajen lalubo dabarun da suka dace da yanayin da take ciki domin amfanawa al’ummarta.

Karkashin shugabancin JKS cikin shekaru 100 da suka gabata, kowa zai iya shaida cewa, kasar Sin ta samu manyan nasarori na ban mamaki da babu wata kasa da ta samu a duniya. Misali na baya-bayan nan shi ne, fatattakar talauci baki daya. Duk da yawan al’ummarta da kuma kasancewarta kasa mai tasowa, Sin ta yi abun da manyan kasashe suka gaza.

LABARAI MASU NASABA

Sin: Amurka Ba Ta Sa Lura Ga Kare Hakkin Dan Adam

Bikin CIIE Ya Nuna Yadda Sin Ke Ba Da Jagora Kan Harkokin Bude Kofa

Ta tabbatar da dukkan al’umominta daga kabilu daban daban na cikin wadata ba tare da barin kowa a baya. Haka kuma, ta tabbatar da cewa ana rayuwa cikin kwanciyar hankali da lumana a tsakaninsu.

Jama’a su suka san matsalolinsu, kuma damawa da su cikin harkokin kasa, shi zai kai ga ci gaban da ake muradi. Wakilan jam’iyyar daga dukkan bangarori, da suka hada da manoma da ma’aikata daga bangarori daban-daban na samun damar wakiltar al’ummominsu yayin taron wakilan jam’iyyar Kwaminis ta kasar, lamarin dake kara jaddada cewa, al’umma ne ke jan ragamar demokradiyyar kasar, kuma wannan tsari ne ya kai ta ga samun dimbin nasarori.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sin: Amurka Ba Ta Sa Lura Ga Kare Hakkin Dan Adam
Daga Birnin Sin

Sin: Amurka Ba Ta Sa Lura Ga Kare Hakkin Dan Adam

November 11, 2025
Bikin CIIE Ya Nuna Yadda Sin Ke Ba Da Jagora Kan Harkokin Bude Kofa
Daga Birnin Sin

Bikin CIIE Ya Nuna Yadda Sin Ke Ba Da Jagora Kan Harkokin Bude Kofa

November 11, 2025
CIIE Ya Kasance Gadar Sada Tattalin Arzikin Kasar Sin Da Na Duniya
Daga Birnin Sin

CIIE Ya Kasance Gadar Sada Tattalin Arzikin Kasar Sin Da Na Duniya

November 11, 2025
Next Post
‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Zamfara, Sun Kashe Mutum Daya, Sun Sace Wasu 8 

'Yan Bindiga Sun Kai Hari Zamfara, Sun Kashe Mutum Daya, Sun Sace Wasu 8 

LABARAI MASU NASABA

Za Mu Kare Sojojin Da Ke Bakin Aiki — Ministan Tsaro

Za Mu Kare Sojojin Da Ke Bakin Aiki — Ministan Tsaro

November 12, 2025
‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 3 Tare Da Sace Babur A Nasarawa

‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 3 Tare Da Sace Babur A Nasarawa

November 12, 2025
‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi Sama Da 200 A Katsina

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi Sama Da 200 A Katsina

November 12, 2025
Injiniya Sagir Ibrahim Ƙoƙi Ya Fice Daga Jam’iyyar NNPP

Injiniya Sagir Ibrahim Ƙoƙi Ya Fice Daga Jam’iyyar NNPP

November 12, 2025
Bayanan Da Muka Samu Sun Nuna An Fara Samun Tsaro A Nijeriya – Hafsan Sojin Ƙasa

Bayanan Da Muka Samu Sun Nuna An Fara Samun Tsaro A Nijeriya – Hafsan Sojin Ƙasa

November 12, 2025
Yadda Ɓarawo Ya Shiga Gidan Gwamnatin Kano Ya Saci Motar Ayarin Mataimakin Gwamna

Yadda Ɓarawo Ya Shiga Gidan Gwamnatin Kano Ya Saci Motar Ayarin Mataimakin Gwamna

November 12, 2025
Zargin Kisan Kiristoci: Dalilan Da Ya Sa Trump Ba Zai Iya Kai Wa Nijeriya Hari Ba

Zargin Kisan Kiristoci: Dalilan Da Ya Sa Trump Ba Zai Iya Kai Wa Nijeriya Hari Ba

November 12, 2025
Coas

Bayan Ganawa Da Tinubu, COAS Ya Tabbatar Wa ‘Yan Nijeriya Samun Ingantaccen Tsaro

November 11, 2025
Sin: Amurka Ba Ta Sa Lura Ga Kare Hakkin Dan Adam

Sin: Amurka Ba Ta Sa Lura Ga Kare Hakkin Dan Adam

November 11, 2025
Bikin CIIE Ya Nuna Yadda Sin Ke Ba Da Jagora Kan Harkokin Bude Kofa

Bikin CIIE Ya Nuna Yadda Sin Ke Ba Da Jagora Kan Harkokin Bude Kofa

November 11, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.