“kasar Sin za ta kara bude kofa ga duniya, kuma manufarta ta yin amfani da jarin waje ba ta sauya ba, kuma ba za ta sauya ba a nan gaba,” cewar shugaban kasar Sin Xi Jinping.
A dai yadda harkokin cinikayya ke neman tabarbarewa a duniya saboda matakai na son zuciya da son kai, irin wannan furuci daga shugaban babbar kasa, abu ne mai kwantar da hankali da bayar da karin kuzari da kyakkyawan fata.
- Sarki Sanusi Ya Yabawa Gwamna Yusuf Kan Manufofin Haɓaka Jama’ar Kano
- Farashin Man Fetur Ya Ƙara Tashi Sakamakon Rikicin Dangote Da NNPCL
Yayin da batun kariyar cinikayya ya yamutsa harkokin kasuwanci a duniya, kasar Sin ta zama karfin dake kokarin tabbatar da daidaito. Kamar yadda shugaba Xi Jinping ya bayyana yayin taron da ya yi da shugabanni da wakilan manyan kamfanonin kasa da kasa a karshen makon da ya wuce, ba tare da la’akari da yanayin da duniya za ta shiga ba, Sin ba za ta sauya manufarta ta bude kofa da hada hannu da sauran kasashe ba.
Cikin shekaru sama da 40 da fara aiwatar da manufar bude kofa da gyare-gyare a cikin gida, kasar Sin ta samu dimbin sakamako na a zo a gani, har ta kai matakin da take bayar da gudunmawar kaso 30 na tattalin arzikin duniya. Ban da haka, duk muna ganin yadda kamfanonin kasashen wajen ke tururuwar shigowa kasar da ma yadda suke fadada zuba jari da ayyukansu a kasar Sin, domin duk ci gaban kasar Sin ta kowacce fuska, dama ce a gare su ta habaka harkokinsu.
Har kullum, Sin ta kasance mai kokarin lalubo hanyoyin saukakawa kamfanonin waje da samar musu da damarmakin raya kansu da samun ci gaba, maimakon matsa musu ko aiwatar da matakan kariyar cinikayya ko kakaba haraji fiye da kima. Idan muka nazarci manufofin kasar Sin, to a nan za mu fahimci abun da ake nufi da “Moriyar Juna”, domin ba don ci gaban kanta kadai take aiwatar da kyawawan manufofinta ba, sai don sauran kasashe ma su ci gajiya. Mun ga yadda take shirya harkokin kasuwanci kamar baje koli daban-daban inda mabambantan kasashe ke hallara su tallata kansu da hajojinsu ba kadai ga al’ummar Sinawa ba, har da na sauran kasashe mahalarta. Za mu iya cewa, ba jigon habaka kasuwanci kadai Sin ta zama ba, ta zama dandalin habaka musaya da cudanya da fahimtar juna tsakanin kasa da kasa da hana duniya tangal-tangal, wadanda abubuwa ne da ake matukar bukata.
Yakin cinikayya ba zai taba durkusar da kasar Sin ba, sai dai kaikayi ya koma kan mashekiya. Yayin da wasu kasashen ke aiwatar da kariyar cinikayya da kokarin rufe kofarsu ga sauran sassan duniya, kasar Sin ta kara bude kofarta, tana kuma maraba da ’yan kasuwa daga kasa da kasa. Maimakon kawo cikas, kasar Sin za ta lalubo hanyoyin samun karin ci gaba ga kanta da sauran sassan duniya, kuma kariyyar cinikayya da ake yi, zai rikide ya zamo alheri a gare ta.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp