Amurka ta kaddamar da bincike kan sabuwar wayar salular da kamfanin sadarwar kasar Sin wato Huawei ya bullo da ita. Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Mao Ning ta amsa tambayar da aka yi mata a yau Jumma’a kan wannan batu, inda ta ce, kasarta na matukar adawa da abun da Amurka take yi, na siyasantar da batutuwan da suka shafi tattalin arziki da cinikayya da kimiyya da fasaha, da wuce gona da iri wajen amfani da ikon kasa.
Jami’ar ta jaddada cewa, sanya takunkumi, ko haifar da tsaiko, ko kuma matsa lamba, duk ba za su hana ci gaban kasar Sin ba, akasin haka, za su karfafa gwiwarta wajen dogaro da kanta, da yin kirkire-kirkire a fannin kimiyya da fasaha. (Murtala Zhang)