Mai magana da yawun ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin ya bayyana cewa, kasar tana matukar adawa da yunkurin Amurka na kara yawan dozin-dozin na kamfanoninta a cikin jerin kamfanonin da aka takaita fitar da kayayyakinsu zuwa kasashen waje.
Jami’in, wanda ya bayyana haka a ranar Larabar nan, ya ce, matakin na Amurka ba komai ba ne illa murkushewa da kuma takura wa wasu kamfanonin kasashen ketare, tare da danne hakkokin sauran kasashen duniya na samun ci gaba. Yana mai cewa, hakan zai yi matukar cutar da kamfanonin tare da kawo cikas ga kwanciyar hankali da samun wadataccen tsarin samar da kayayyaki a duniya.
Ya kara da cewa, matakin zai yi kafar ungulu ga kokarin warware matsaloli ta hanyar tattaunawa da hadin gwiwa, kuma kasar Sin tana kira ga Amurka da ta gaggauta kawo karshen kurakuran da take tafkawa, kana ya ce, kasar za ta dauki matakan da suka dace don kiyaye hakkoki da muradun kamfanonin Sinawa. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp