Kasar Sin ta bayyana adawa kan takunkuman da Amurka ta kakabawa kamfanoninta bisa dalilai masu alaka da Rasha.
Yayin taron manema labarai na yau Litinin, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Mao Ning, ta shaidawa manema labarai cewa, matakin na Amurka, wanda ba shi da madogara da dokokin kasa da kasa ko sahalewar kwamitin sulhu na MDD, wani yunkuri ne da ya fita daga huruminta, haka kuma ya saba da muradun kasar Sin.
Ta kara da cewa, kasar Sin za ta tsaya ne kan matsayinta na sanin ya kamata da kin goyon bayan wani bangare dangane da rikicin Ukraine, haka kuma za ta yi kokarin ingiza hawa teburin sulhu domin warware batun a siyasance, yayin da Amurka ke rura wutar rikicin ta hanyar zuba tallafin ayyukan soji na dala biliyan 32 a fagen daga.
Mao Ning ta kuma yi kira ga Amurka, ta daina yada labaran bogi, kana ta soke takunkumanta kan kamfanonin Sin, tare da bin turbar da ta dace na sassauta rikicin.