A yau Asabar, ma’aikatar harkokin wajen Sin ta sanar da cewa, kasar na adawa da matakin Amurka na rattaba hannu kan kudurin doka game da yankin Xizang(Tibet), tana mai cewa Sin ta riga ta gabatar da korafinta ga Amurka.
Shugaban Amurka Joe Biden, ya rattaba hannu kan dokar da Amurkar ke kira da “Dokar Samar da Mafita ga Rikicin Tibet da Sin” a jiya Juma’a. Dokar dai na amincewa ne da batun “Greater Tibet” da kungiyar Dalai ta kirkiro, tare da neman gwamnatin Amurka da manzon musammam kan batutuwan Tibet, da su karyata abin da suke kira wai “labaran bogi game da Tibet” dake fitowa daga gwamnatin kasar Sin.
- Fahimtar Manufar Kasar Sin Ta Yin Kwaskwarima A Sabon Zamani
- Shugaba Bola Tinubu Zai Yi Sauye-Sauye A Gwamnatinsa Kwanan nan
Cikin wata sanarwa, shugaban na Amurka ya ce “dokar bata sauya dadaddiyar manufar kasar ta amincewa da yankin Tibet mai zaman kanta da sauran yankunan Tibet a matsayin wani bangare na Jamhuriyar Jama’ar Kasar Sin ba”.
A cewar kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin, dokar ta sabawa dadadden matsayi da alkawarin gwamnatin Amurka da ka’idojin huldar kasa da kasa, haka kuma ta yi matukar yin katsalandan cikin harkokin gidan Sin, lamarin dake tsaiko ga muradun Sin da ma aikewa da mummunan sako ga masu neman ‘yancin yankin Tibet. Ya ce Kasar Sin na adawa da hakan, kuma ta gabatar da korafinta ga Amurka.