Ranar 2 ga watan Fabrairun wannan shekara ita ce ranar dausayi ta duniya ta 29. Jigon ranar dausayi ta duniya ta bana shi ne “Kare dausayi, gina kyakkyawar makoma tare”.
Wakilinmu ya samu labari daga hukumar kula da gandun daji da ciyayi ta Sin cewa, a shekarun baya-bayan nan, kasar Sin na ci gaba da inganta kiyaye dausayi da maido da su, kuma an kyautata yanayin muhalli na muhimman wuraren dausayi yadda ya kamata.
- Gwamna Buni Ya Jaddada Bai Wa Sojoji Gudunmawar Kawo Karshen Boko Haram
- Ba Za Mu Daina Kera Makaman Nukiliya Ba – Kim Jong Un
Bayanai na baya-bayan nan daga hukumar kula da gandun daji da ciyayi ta kasar sun nuna cewa, tun daga shekarar 2012, kasar Sin ta aiwatar da ayyukan kiyaye dausayi fiye da 3,700, da farfado da dausayi sama da hekta miliyan 1, kana fadin yankin dausayi ya zarce da hekta miliyan 56.35 a kasar, da kuma kafa yankunan kare dausayi iri iri fiye da 2200.
Ban da haka kuma, an kara saurin aiwatar da ayyuka na musamman na kare da maido da mangrove, wanda ya sa fadin mangrove ya kai hekta 30300, adadin ya karu da kusan hekta 8300 daga farkon karnin da muke ciki, wanda ya sa kasar Sin ta kasance daya daga cikin kasashe kalilan a duniya wadanda suka samu karuwar yankin mangrove.
Bugu da kari, shekarar bana ita ce shekarar da ta cika shekaru 20 da kafuwar wuraren shan iska na dausayi na kasar ta Sin. A cikin shekaru 20 da suka gabata, wuraren shan iska na dausayi na kasar sun yi nasarar kare dausayi hekta miliyan 2.4 yadda ya kamata a fadin kasar.(Safiyah Ma)