Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya fadawa taron manema labaru na yau da kullum Jumma’ar nan cewa, kasar Sin tana da cikakken kwarin gwiwa wajen cimma burin da aka sanya a gaba na “dakile annoba, da daidaita tattalin arziki, da tabbatar da samun ci gaba yadda ya kamata”.
A jiya ne aka ba da rahoton cewa, jakadan Amurka dake kasar Sin, ya soki manufofin kasar Sin na dakile annobar COVID-19 da zarar an gano ta a wani taro, yana mai cewa, wannan mataki na shafar zuba jarin waje.
A kan wannan batu, Wang Wenbin ya bayyana cewa, manufar matakin da gwamnatin kasar Sin ta bullo da shi game da tsarawa da aiwatar da babbar manufar kawar da cutar da zarar an gano da, ita ce mayar da batun tsaro da lafiyar mutane fiye da biliyan 1.4 a gaban komai. Daga watan Janairu zuwa watan Mayu, yawan shigi da ficin kayayyaki na kasar Sin, ya karu da kashi 8.3 bisa dari kan makamancin lokaci na bara, yayin da jarin waje ya karu da kashi 17.3 bisa dari a kan na shekarar da ta gabata.
Wadannan alkaluma sun nuna hakikanin yadda masu zuba jari na kasashen waje suke son zuba jari a kasar Sin, da cikakken imaninsu kan ci gaban tattalin arziki da zamantakewar kasar.
Wannan ya kara nuna cewa, matakan kandagarki da hana yaduwar cutar masu inganci, su ne tushen ci gaban tattalin arziki da zamantakewa da kuma kyakkyawan muhalli na yin kasuwanci.(Ibrahim)