Kasar Sin na goyon bayan samar da tallafi mai dorewa na isassun kudi ga ayyukan wanzar da zaman lafiya na Tarayyar Afrika (AU).
Wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Fu Cong ne ya bayyana haka yayin wata budaddiyar muhawara ta kwamitin sulhu na majalisar a jiya Lininn.
- Xi Jinping Ya Taya Murnar Ranar Malamai Ta Kasar Sin
- Samar Da Asibitin Koyarwa A Lafiya Cigaba Ne Ga Jihar Nasarawa – Dr Ikrama
A cewar Fu Cong, bunkasa karfin nahiyar na tabbatar da tsaro da zaman lafiya da kanta, da kara mara baya ga tsare-tsaren shiyyoyin nahiyar, alkibla ce mai muhimmanci a aikin yi wa shirin wanzar da zaman lafiya na MDD garambawul.
Da yake tsokaci kan taron dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afrika (FOCAC) da aka yi makon da ya gabata a Beijing, ya ce cikin shekaru 3 masu zuwa, kasar Sin za ta hada hannu da nahiyar Afrika wajen aiwatar da shirye-shiryen hadin gwiwa 10 kan zamanintar da bangarorin biyu, ciki har da shirin hadin gwiwa na samar da tsaro na bai daya.
Ya ce kasar Sin za ta dauki matakan da suka dace na taimakawa kasashen Afrika inganta karfinsu na soji da tsaron kasa da bayar da horon ga sojoji da ’yan sanda da sauran jami’an tsaro, domin tabbatar da nahiyar ta kawar da hadarin nakiyoyi baki daya. (Mai Fassara: Fa’iza Mustapha)