Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana a yau cewa, kasar na goyon bayan tsarin wanzar da zaman lafiya a kasar Colombia, tare da yabawa kokarin bangarori masu ruwa da tsaki na ganin tabbatuwar hakan.
Kakakin ma’aikatar ne ya bayyana hakan a yau Asabar, bayan a farkon wannan mako, gwamnatin Colombia da dakarun ‘yantar da kasar na ELN sun sanar da dakatar da bude wuta na tsawon kwanaki 180 a fadin kasar. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp