Ma’aikatar kula da albarkatun ruwa ta kasar Sin, ta ce ta matsa kaimi wajen samar da ruwa ga kimanin manya da matsakaitan yankuna 500 da ake ban ruwa, a yankuna masu fama da fari dake kudu maso yammacin kasar.
Zuwa yanzu, an kai jimillar cubic mita miliyan 160 na ruwa zuwa yankunan dake fama da fari, wadda ke samar da ruwa ga gonakin da jimillarsu ta kai sama da mu miliyan 3.5 ko kadada 230,000.
Baya ga haka, kasar Sin ta ware yuan miliyan 174 kimanin dala miliyan 24.49, domin inganta yaki da fari da tabbatar da wadatar ruwa. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp