Ma’aikatar harkokin wajen Sin ta ce kasar na maraba da kamfanonin kasashen waje su yi amfana tare da cin gajiyar damarmakin da ci gaban kasar ya kawo.
Kakakin ma’aikatar Mao Ning ce ta bayyana haka yayin taron manema labarai na yau Alhamis, lokacin da aka yi mata tambaya game da wata mukala da jakadan Japan a kasar Sin, Kanasugi Kenji ya rattabawa hannu, inda ya ce kasar Sin ta yi gaba sosai a fannonin kera motocin masu amfani da lantarki da kirkirarriyar basira da tattalin arziki na dijital da ayyukan kare muhalli.
Jakadan ya kara da cewa, ba za a iya raba ci gaban tattalin arzikin Japan da ma na duniya da tattalin arzikin Sin ba, yana cewa, ya kamata Japan ta yi amfani da damarmakin dake tattare da ci gaban tattalin arzikin kasar Sin. (Fa’iza Mustapha)