Yauzu haka, tattalin arzikin duniya na ci gaba da fuskantar matsin lambar da sauye-sauyen yanayin duniya da annobar COVID-19 suka haifar, lamarin da ya sa ake mai da hankali sosai kan yanayin raya tattalin arziki a kasar Sin, wadda ta kasance abokiyar ciniki mafi muhimmanci ta kasashe da yankuna fiye da 120.
Matakan da kasar ta dauka wajen tinkarar annobar COVID-19 sun ba ta damar dakile yaduwar cutar gami da raya bangaren samar da kayayyaki. Kana yadda kasar take kokarin magance samun masu kamuwa da cutar COVID-19, ya sa ta iya kiyaye wani yanayin tattalin arziki da na zaman al’umma mai karko, ba tare da salwantar da kudi da kayayyaki, da karfin mutane ba.
- Masanin Huldar Kasa Da Kasa A Jami’ar Abuja: Kasar Sin Na Sa Kaimi Ga Sabon Nau’in Dunkulewar Duniya
Ban da haka, yadda kasar Sin take fitar da karin kayayyaki zuwa kasuwannin ketare, ya sa kasashen yamma irinsu Amurka da Birtaniya ke iya gudanar da harkokinsu yadda suke bukata.
Matakan hana yaduwar cutar COVID-19 da kasar Sin ta dauka suna taimakawa tabbatar da ingancin ayyukan samar da kayayyaki a kasar, ta yadda kasar ke samar da dimbin gudunmawa wajen biyan bukatun kasashe daban daban na samun isassun kayayyaki masu alaka da kandagarkin yaduwar cuta, da masana’antu, da zaman rayuwar jama’a ta yau da kullum.
Wasu alkaluman da ma’aikatar kasuwancin kasar Sin ta gabatar sun nuna cewa, kasashen Amurka da Japan da Koriya ta Kudu, da Jamus sun zuba mafi yawan jari ga kasar Sin. Ta la’akari da muhimmiyar rawar da wadannan kasashe ke takawa a fannin tattalin arzikin shiyyoyinsu, za a iya ganin tasirin tattalin arizkin Sin a duniya.
Haka zalika, a kwanan baya, asusun ba da lamuni na duniya IMF ya sanar da daga matsayin kudin Sin RMB cikin kudin kasashe daban daban da ake iya biyan bashin asusun da shi na SDR, daga kaso 10.92 zuwa kaso 12.28.
Wannan ma ya nuna yadda gamayyar kasa da kasa suke da cikakken imani kan tattalin arziki da kasuwar hada-hadar kudi na kasar Sin. (Bello Wang)