Shugaban babban zauren MDD na 79 Philemon Yang, ya ce kasar Sin ta bayar da gaggarumar gudunmuwa ga wanzuwar zaman lafiya da ci gaba mai dorewa a duniya, a matsayinta na mambar dindindin a Kwamitin Sulhu na MDD, kuma kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya.
Philemon Yang ya bayyana haka ne yayin hirar da ya yi a baya bayan nan da kamfanin dillancin labarai na kasar Sin, Xinhua.
Ya kuma kara da cewa, yana fatan kasar Sin za ta ci gaba da goyon bayan karfafa rawar da MDD ke takawa cikin harkokin kasa da kasa da farfado da tsarin cudanyar bangarori daban-daban, domin shawo kan kalubale na bai daya da kasa daya tilo ba za ta iya ba a wannan zamani.
Ya kuma jadadda cewa, dorewar daraja da kimar MDD ta dogara ne ga raya tsarin diplomasiyya maimakon rikici, da kuma kiran da take yi na a hada hannu wajen samar da adalci da zaman lafiya da tsaro a duniya, yana mai fatan kasa da kasa za su ci gaba da zama masu kwarin gwiwa da hadin kai da kiyaye ka’idoji, ta yadda zuri’o’i masu zuwa za su ci gajiya. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp