Kasar Sin ta bayyana matukar rashin gamsuwa da matakin kasar Amurka na kara haraji kan wasu kayayyakin da take fitarwa, ciki har da motoci masu amfani da lantarki da kananan kayayyakin laturoni na Chip da kayayyakin kiwon lafiya.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da ma’aikatar kula da harkokin cinikayya ta kasar Sin ta fitar a yau Talata. Sanarwar ta kara da cewa, ya kamata Amurka ta gaggauta gyara kuskurenta, ta kuma soke harajin da ta karawa kasar, tana mai cewa, kasar Sin za ta dauki matakan da suka wajaba na kare hakkoki da muradunta.
- Kotu Ta Daure Wani Mutum Wata 2 A Gidan Yari Kan Satar Doya
- Sin Ta Kalubalanci Amurka Da Ta Samar Da Kyakkyawan Yanayin Hadin Gwiwa Kan Tinkarar Sauyin Yanayi Da Kyautata Tsarin Raya Tattalin Arzikin Duniya Ba Tare Da Gurbata Muhalli Ba
A yau Talata, fadar White House ta kasar Amurka ta sanar da kakaba sabbin haraji kan motoci masu amfani da lantarki da batura masu aiki da hasken rana da sauran kayayyaki masu amfani da makamashi mai tsafta na kasar Sin dake shiga kasar, a wani yunkuri na kariyar cinikayya da aka yi amana zai kasance hadari ga burin Amurka na karfafa takara da rage fitar da hayakin Carbon.
Bisa shirin, haraji kan motoci masu amfani da lantarki na kasar Sin zai karu daga kaso 25, zuwa kaso 100. Haka kuma, akwai wani karin kaso 2.5 na haraji kan dukkan ababen hawa da suka shiga kasuwar Amurka, inda jimilar haraji kan motoci masu amfani da lantarki na kasar Sin ta kai kaso 102.5.
Akwai yiwuwar sabon harajin da aka kara wani mataki na gwamnatin Biden na nuna matsi kan kasar Sin yayin da yakin neman zaben shugabancin kasar ya kara zafi. (Fa’iza Mustapha)