Hukumar kula da ‘yan sama jannati na kasar Sin (CMSA), a yau Laraba, ta bayyana sunayen tufafin ‘yan sama jannati da motar zirga-zirga a duniyar wata na aikin binciken wata na kasar.
CMSA ta ce, an sa ma tufafin na ‘yan sama jannati suna Wangyu, wanda ke nufin kallon duniyar sama, kuma ya yi daidai da sunan tufafin da ‘yan sama jannati su kan sa lokacin da suka fita daga tashar sararin samaniya, wato Feitian, wanda ke nufin tashi zuwa sararin samaniya.
- Wata Ɗalibar Kwalejin Fasaha Ta Tarayya Da Ke Bauchi Ta Rasa Ranta A Haɗarin Mota
- Yawan Motocin Da Sin Ta Fitar Zuwa Ketare A 2024 Ya Karu Da Kaso 23%
Kazalika, sunan motar zirga-zirga a duniyar wata shi ne Tansuo, wanda ke nufin binciken gaibu. Hukumar ta ce, wannan sunan yana nuna aikin da motar ke yi, da darajarta wajen taimaka wa jama’ar kasar Sin wajen gano ababen al’ajabi na duniyar wata.
A halin yanzu, ayyukan bincike da suka shafi Wangyu da Tansuo suna ci gaba yadda ya kamata, a cewar CMSA. (Mohammed Yahaya)