Mataimakin wakilin Sin na dindindin a MDD Geng Shuang, ya yi kira ga Amurka ta daina shafawa wasu kashin kaji da ingiza Ukraine ta takali fada.
Geng Shuang ya bayyana haka ne jiya ga taron Kwamitin Sulhu na MDD, yana cewa, tun bayan barkewar rikicin, Sin take ta kira ga bangarorin da su tsagaita bude wuta, su hau teburin sulhu da maido da zaman lafiya, kuma kasashe da dama sun yi maraba da rawar da Sin ke takawa da gudunmuwarta wajen warware batun na Ukraine.
- Kirsimeti: NSCDC Za Ta Jibge Jami’ai 3,542 A Kano
- Uwargidan Shugaban Kasa Ta Yi Rabon Tallafi Ga Tsofaffi A Jihar Kogi
Ya kara da cewa, Amurka ce kasa daya tilo da ta zabi ta yi watsi da kokarin Sin tare da ci gaba da yada karairayi.
Ya ce, fatansu shi ne, Amurka ta dakatar da rashin hankalin da take yi na shafawa wasu kashin kaji da yin fito-na-fito. Bugu da kari, ya bukaci Amurka ta hada hannu da kasashe masu ruwa da tsaki, ciki har da Sin domin hada hannu da cimma matsaya da samar da sharudda da yanayi mai dacewa da warware batun Ukraine. (Fa’iza Msutapha)