A jiya Juma’a ne wakilin kasar Sin a MDD ya bukaci Isra’ila da ta aiwatar da kudurin MDD game da tsagaita bude wuta a zirin Gaza daga dukkan fannoni, yana mai cewa, abu mai ban tausayi da ke faruwa a Gaza ya zama gwaji ga lamirin bil Adama da kuma amincin kwamitin sulhu na MDD.
Mukaddashin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Dai Bing ya bayyana a kwamitin sulhu na MDD a jiya Juma’a cewa, mun bukaci Isra’ila da ta gaggauta aiwatar da kudurin, da kuma dakatar da hare-haren soji da take kaiwa Gaza, da azabtar da fararen hular Gaza.
- Kasar Sin Ta Ba Da Taimakon Jinya Kyauta Ga Mafiya Rauni Miliyan 250 A shekarar 2023
- Kasar Sin Na Allah Wadai Da Harin Da Aka Kai Wa Ma’aikatan Agaji Na Kasa Da Kasa A Gaza
Ya yi tir da harin da Isra’ila ta kai wa motocin jigilar kayayyakin jin kai, ya kuma bukaci Isra’ila da ta mutunta dokokin kasa da kasa da kuma dokokin jin kai na kasa da kasa, da dakatar da kai hare-hare kan hukumomin jin kai da ma’aikata, tare da ba da hadin kai ga hukumomin jin kai don kai agaji.
Dai dai ya jaddada cewa, ta hanyar aiwatar da tsarin samar da “kasashe guda biyu” daga dukkan fannoni da kuma kafa kasar Falasdinu mai cin gashin kanta ne, yankin zai iya fita daga cikin mummunan yanayi, inda Isra’ila da Falasdinu suke ta yin rikici a tsakaninsu. Ya nanata matsayin kasar Sin kan goyon bayan Falasdinu ta zama mamban MDD a hukumance, kana ya bukaci kwamitin sulhun da ya dauki mataki cikin gaggawa.
Kwamitin kare hakkin dan Adam na MDD a jiya Juma’a ya zartas da wani kudiri na neman a dorawa Isra’ila alhakin aikata laifukan yaki da kuma cin zarafin bil’Adama a zirin Gaza. Kudirin ya kuma bukaci dukkan kasashen duniya da su dakatar da sayarwa, da mikawa, da kuma karkatar da makamai da alburusai da sauran kayan aikin soji ga Isra’ila.
Daga cikin kasashe 47 da ke cikin kwamitin, wasu 28 ne suka kada kuri’ar amincewa, 13 ba su kada kuri’a ba, yayin da wasu 6 suka ki amincewa da kudirin. Kasar Sin ta goyi bayan kudirin, yayin da Amurka da Jamus suka nuna adawa da shi. (Yahaya)