Kasar Sin ta ce ba za ta taba mantawa da rashin imanin kungiyar tsaro ta NATO na kai harin bam kan ofishin jakadancinta dake Belgrade a shekarar 1999 ba, lamarin da ya yi sanadin mutuwar Sinawa ‘yan jarida 3, da raunata wasu Sinawa jami’an diflomasiyya su 20.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Wang Wenbin, ya bayyana a yau cewa, kasar ba za ta taba mantawa da jini da rayukan da aka sadaukar wajen tabbatar da gaskiya da adalci ba.
Kakakin ya bukaci kungiyar NATO da kawayenta su waiwayi muggan laifukan da suka aikata, su yi watsi da ra’ayin yakin cacar baka, su kuma daina neman fito-na-fito.
Ya kuma yi kira ga kungiyar da ta dauki kwararan matakai wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Turai da ma duniya baki daya. (Fa’iza)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp