Ma’aikatar kula da muhallin halittu ta kasar Sin ta gudanar da taron manema labarai a yau Litinin 24 ga wata, inda wani jami’inta ya nuna cewa, ingancin iska da muhallin kasar sun kyautatu a shekarar da ta gabata, lamarin da ya shaida cewa, kasar Sin ta cimma burin magance gurbatar yanayi a shekara ta 2024.
Jami’in ya kara da cewa, a shekara ta 2024, yawan kwanakin da aka samu kyakkyawan ingancin iska ya kai kaso 87.2%, adadin da ya karu da kaso 1.7% idan aka kwatanta da na shekara ta 2023. Kazalika, yawan kwanakin da aka samu mummunar gurbatar yanayi ko fiye da haka, ya kai kaso 0.9%, adadin da ya ragu da kaso 0.7%. A Beijing, wato fadar mulkin kasar Sin kuma, ingancin iska ya dauki matsayin kasa na biyu cikin shekaru 4 a jere, inda har kullum a kan samu kyakkyawan yanayi. (Murtala Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp