Kwanan nan ne kasar Sin ta wallafa rahoton kare hakkin dan Adam na shekara-shekara na 2024, wanda shi ne mujalladi na 14 tun da kungiyar nazarin hakkin dan Adam ta kasar Sin, wato babbar kungiyar masana ta kasa da ta sadaukar da kai wajen gudanar da bincike kan hakkin dan Adam a kasar Sin ta fara wallafa shi a shekarar 2011.
A bisa bincike mai zurfi, rahoton ya yi amfani da cikakkun bayanai da kuma kararraki daban-daban don bayyana ci gaban da aka samu a kokarin da kasar Sin ta yi na kare hakkin dan Adam a shekarar 2023. (Yahaya)