Ofishin Yada Labarai na Majalisar Gudanarwar Kasar Sin ya fitar da takardar bayani mai taken “Batun kaiwa kololuwar fitar da hayakin zuwa shekarar 2030, da kuma kawar da illar sa zuwa shekarar 2060: Tsare-tsare da Samar da Mafita na Kasar Sin.”
Takardar ta gabatar da cikakken bayani game da manyan nasarorin da kasar Sin ta samu a kan kaiwa kololuwar fitar da hayakin zuwa shekarar 2030, da kuma kawar da illar sa zuwa shekarar 2060 a cikin shekaru biyar da suka gabata, kuma ta bayyana hanyoyin da take bi, da ayyuka da kuma gogewarta a wannan fannin.
Takardar ta kuma yi magana game da batun sauyin yanayi a matsayin kalubalen da ke shafar dukkan bil’adama, wanda ke bukatar gudunmawar kowa da kowa da kuma daukar matakai na hadin gwiwa. Ta hanyar jajircewarta ga bin tsarin bangarori masu yawa da hadin gwiwar kasashen duniya, kasar Sin tana shimfida sabuwar hanya wajen kula da harkokin sauyin yanayi a duniya. Kazalika, bisa la’akari da rayuwar gaba, kasar a shirye take ta hada karfi da karfe tare da kasashen duniya domin habaka tattalin arziki mai kiyaye lafiyar muhalli, da karfafa ci gaba mara illata muhalli, da magance kalubalen sauyin yanayi a duniya da kuma kare duniyar, tare da tabbatar da cewa duniya ta kasance mai tsabta da kuma kyawun gani. (Abdulrazaq Yahuza Jere)













