Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana a yau Laraba cewa, kasar na matukar adawa da yunkurin Amurka na samar da tallafin soji ga yankinta na Taiwan, haka kuma ta gabatar da korafi mai karfi ga bangaren Amurka.
Da take bayyana Taiwan a matsayin muhimmin cikin muradun kasar, haka kuma jan layin da ba ta amince a keta ba a dangantakarta da Amurka, kasar Sin ta bukaci Amurkar ta martaba manufar kasancewar Sin daya tak a duniya, da sanarwowi 3 dake tsakaninsu, ta daina inganta tuntuba dangane da batun soji tsakaninta da yankin Taiwan, ko kuma samarwa yankin makamai ta kowacce hanya da kuma fuska, kana ta daina kirkiro abubuwan da ka iya kara zaman dardar a mashigin tekun Taiwan da daina hada baki da goyon bayan masu neman ‘yancin yankin na Taiwan da karfin tuwo.
A baya-bayan nan ne shafin yanar gizo na fadar White House ya sanar da cewa, Amurka za ta samar da kimanin dalar Amurka miliyan 345 na tallafin soji ga yankin Taiwan na kasar Sin. (Fa’iza Mustapha)