Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya gabatar da shawarwari 5 na kasar Sin don gane da warware batun nukiliyar kasar Iran ta hanyar da ta dace.
Wang Yi ya bayyana shawarwarin ne yau Jumma’a a nan birnin Beijing, yayin ganawarsa da mataimakin ministan harkokin wajen Rasha, Ryabkov Sergey Alexeevich da mataimakin ministan harkokin wajen Iran, Kazem Gharibabadi.
- Yadda Nijeriya Ta Zarce Yawan Man Da OPEC Ta Ware Mata – Bincike
- Me Ya Sa Jama’ar Turai Ke Adawa Da Sayen Kayayyaki Kirar Amurka?
Da farko, ya ce kasar Sin na nacewa ga warware rikice-rikice cikin lumana ta hanyoyin siyasa da diplomasiyya, kuma tana adawa da amfani da karfi da kuma takunkuman da ba su dace ba.
Na biyu, Sin tana tsayawa tsayin daka kan tabbatar da daidaiton hakkoki da nauye-nauye, da daukar ingantaccen mataki wajen cimma burin kawar da yaduwar nukiliya da amfani da makamashin nukiliya ta hanyar da ta dace.
Na uku, Sin tana nacewa ga aiwatar da tsarin yarjejeniyar nukiliya ta Iran, a matsayin tushen cimma sabuwar matsaya.
Na hudu, kudurin Sin shi ne inganta hadin gwiwa ta hanyar tattaunawa, tare da adawa da neman kwamitin sulhu na MDD ya shiga tsakani.
Bugu da kari, ministan ya ce Sin za ta tsaya kan dabarar daukar matakai daya bayan daya da saka alheri da alheri, da neman cimma matsaya ta hanyar tattaunawa. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp