Ministan ilimi na kasar Sin Huai Jinpeng ya shaidawa manema labarai cewa, kasar Sin ta gina tsarin ilimi da babu kamarsa a duniya, kuma matakin zamanantar da ilimi baki daya na kasar, ya shiga matsakaici da ma na sama da shi a kasashen duniya, tare da shimfida tsarin ilimi mai karfi da zai kai ga gina tsarin ilmi mai inganci a fadin kasar.
A cikin shekaru 10 da suka gabata, kasar Sin ta cimma nasara a tarihi a fannin yada ilimi a kowane mataki da nau’in ilimi, kuma a sannu hankali an inganta tsarin ba da ilimi mai sauki ga al’ummar da yawanta ya kai sama da biliyan 1.4.
A halin yanzu, yawan jama’ar kasar Sin da suka samu ilimi mai zurfi ya kai miliyan 240, kuma matsakaicin adadin shekarun ilimi na sabbin ma’aikata ya kai shekaru 14. Ilimi mai zurfi ya ba da gudummawa ga manyan sauye-sauye a tsarin ingancin ma’aikatan kasar Sin. (Mai Fassarawa: Ibrahim Yaya)