Kasar Sin tana goyon bayan hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya wato IAEA, wajen taka rawar da ta dace a kokarin sa kaimi ga cimma matsaya ta siyasa da diflomasiyya kan batun nukiliyar kasar Iran.
Zaunannen wakilin kasar Sin a hukumar ta IAEA Li Song ne ya bayyana hakan a jiya Alhamis, bayan wata ganawar hadin gwiwa da babban darektan hukumar Rafael Grossi, da takwaransa na kasar Rasha Mikhail Ulyanov, da kuma takwaransa na kasar Iran Reza Najafi.
- Rashin Wutar Lantarki: Jihohin Kano, Katsina Da Jigawa Na Samun Wutar Awa 2 Ne Kacal A Kullum
- An Sako Malamin Kiristan Cocin Katolika Da Aka Sace AÂ Kaduna
Kazalika, kasashen Sin, Rasha, da Iran sun jaddada cewa, huldar siyasa da diflomasiyya bisa mutunta juna su kadai ne hanya daya tilo da ta dace kuma mai amfani wajen warware batun nukiliyar Iran. Kana kasashen 3 sun amince cewa, hukumar ta IAEA da babban darektanta na da damar da ta dace da kuma kwarewa wajen ba da gudummawa mai ma’ana ga wannan tsari, da nufin tallafawa kokarin da ake yi na diflomasiyya, da magance matsala ta hanya mai kyau kuma a aikace.
Li ya kara da cewa, Sin da Rasha sun bayyana goyon baya ga Iran wajen karfafa tattaunawa da hadin gwiwa da hukumar IAEA. (Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp