Da safiyar yau Lahadi, aka kammala karo na 3 na bitar katafaren taron dake karatowa, albarkacin cika shekaru 80 da al’ummar Sinawa suka yi nasara a yakin turje wa kutsen Japanawa da karshen yakin duniya na II.
An gudanar da bitar ne a dandalin Tian’anmen dake kwayar birnin Beijing, daga karfe 5 na yammacin jiya Asabar, zuwa 5 na safiyar yau.
Mashirya bitar sun bayyana ta a matsayin ta karshe da ta kunshi bitar dukkan shirye-shiryen da za za gabatar. Kana ta mayar da hankali kan gwajin hadin gwiwar dake tsakanin dukkan bangarorin shirye-shiryen da shimfida tubali mai karfi na nasarar taron.
An gabatar da dukkan shirye-shirye bisa tsari da inganci kuma ba tare da tangarda ba, inda aka cimma dukkan abubuwan da ake buri.
An shirya gudanar da katafaren taron wanda zai kunshi faretin soja ne a ranar 3 ga watan Satumba. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp