An gudanar da taron kolin nazarin ayyukan tattalin arziki na shekara-shekara a Beijing daga ranar Laraba zuwa ta Alhamis, yayin da shugbannin kasar Sin suka tsara tsarin tattalin arziki a shekarar 2025.
Taron kolin nazarin ayyukan tattalin arziki shi ne mafi girman matakin nazarin yanayin tattalin arziki na shekara-shekara kuma shi ne taron yanke shawara a kasar Sin, kuma kasashen waje suna kallonsa a matsayin mafi karfin ma’auni wajen yin hukunci kan manufofin sassan tattalin arziki na kasar Sin a sabuwar shekara. (Mohammed Yahaya)