Kasar Sin ta yi nasarar harba wani sabon makamin roka zuwa sararin samaniya, daga cibiyar harba tauraron dan adam ta Jiuquan dake yankin arewa maso yammacin kasar.
An harba rokar Zhuque-2 ce yau da misalin karfe 9 na safe agogon brining Beijing, kuma ta shiga cikin falaki kamar yadda aka tsara.
Shi ne karo na 2 da aka yi amfani da rokar Zhuque-2 a fannin aikin binciken sararin samaniya. (Ibrahim Yaya)