Rokar Lijian-1 Y4 (ko Kinetica-1) na kasar Sin mai gudanar da ayyukan yau da kullum, ta yi nasarar harba taurarin dan Adam 5 zuwa falakinsu a yau Laraba.
Rokar wadda kamfanin CAS Space na kasar Sin ya kera, ta harba taurarin ne da misalin karfe 7:33 na safe agogon Beijing, daga tashar harba tauraron dan Adam ta Jiuquan dake arewa maso yammacin kasar Sin.
Biyu daga cikin taurarin su ne za su kasance na farko cikin rukunin taurarin dan Adam na AIRSAT na kamfanin, kana sauran 3, za su gudanar da ayyukan da suka hada da nazarin kasa da na yanayi da sauran fannoni.
Wannan ne karo na 4 da wannan nau’in roka ya gudanar da irin wannan aiki. (Fa’iza Mustapha)