Da jijjifin safiyar yau Laraba ne aka harba rukunin taurarin dan’adam masu karamin zango daga doron kasa guda 18 a cikin roka kirar Long March-8 Y6, daga cibiyar harba kumbo ta kasuwanci ta lardin Hainan da ke kudancin kasar Sin.
Taurarin na dan’adam da aka harba, wanda rukuninsu shi ne na biyar a cikin nau’o’insa, sun shiga falakin da ake so cikin nasara, kamar yadda hukumar kula da kimiyya da fasahar sararin sama ta kasar Sin (CASC) ta bayyana. Hukumar ta kara da cewa, taurarin za su kasance rukunin taurarin dan’adam na kaddamar da ayyukan intanet na kasuwanci na kasar Sin.
Wannan aiki na bincike da aka kaddamar na farko daga sashe mai lamba ta 1 na tashar harba kumbon, bayan wanda aka kaddamar a sashen tashar mai lamba ta 2, a ranar 30 ga watan Nuwamban 2024, ya nuna yadda aka kimtsa tsaf a tagwayen shirye-shiryen da tashar sararin samaniya ta farko ta kasuwanci ta kasar Sin ke yi domin gudanar da ayyuka na gaba. (Mai Fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp