Da safiyar Lahadin nan ne, kasar Sin ta yi nasarar harba wani sabon tauraron dan Adam zuwa sararin samaniya, ta hanyar amfani da rokar Long March-4B
An harba sabon tauraron dan Adam na Fengyun-3 07 ne, da misalin karfe 9 da mintuna 36 na safe agogon birnin Beijing, daga cibiyar harba tauraron dan Adam ta Jiuquan dake arewa maso yammacin kasar Sin, kuma nan da nan ya shiga falakinsa kamar yadda aka tsara.
Tauraron dan Adam din, zai rika samar da hidimomi kan hasashen yanayi, da rigakafin bala’i da magance matsalar sauyin yanayi da kiyaye muhalli.
A cewar cibiyar harba taurarin, wannan shi ne karo na 471 da aka yi amfani da rokar Long March, wajen aikin harba taurarin dan Adam zuwa sararin samaniya. (Ibrahim)