Daga shekarar 2021 zuwa ta 2025, kasar Sin ta sake ginawa, da gyara ko kuma fadada wasu zaurukan tunawa da tarihi guda 15, da inganta zaurukan baje kolin kayayyakin tarihi guda 68, domin tunawa da nasarar da kasar ta samu kan zaluncin Japanawa.
Bisa irin wannan kokari, an kafa tsarin dandali na tunawa da tarihi, kamar yadda mataimakin shugaban hukumar kula da al’adun gargajiya ta kasar Sun Deli ya bayyana, a yayin wani taron manema labarai da ya gudana a yau Lahadi, kan al’amuran da suka shafi bikin cika shekaru 80 da samun nasarar yakin turjiyar jama’ar kasar Sin kan zaluncin Japan da kuma yaki da mulkin danniya a duniya.
Sun ya kara da cewa, an tabbatar da fiye da kayayyakin al’adu da ba za a iya motsawa ba guda 10,000 da kuma wadanda za a iya motsawa guda 160,000 da suke da nasaba da yakin a duk fadin kasar Sin. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp