Alkaluman da ma ‘aikatar kasuwancin kasar Sin ta gabatar sun nuna cewa, a watannin Janairu da Fabrairun bana, an kafa sabbin kamfanoni masu jarin kasashen waje har 7160 a kasar Sin, inda yawan su ya karu da kashi 34.9% bisa na makamancin lokacin bara. Kana yawan jarin waje da aka zuba wa kasuwannin kasar cikin watannin 2, ya kai dalar Amurka biliyan 29.8.
Idan an raba kudin bisa sana’o’in da aka zuba wa jari, za a ga yawan kudin da masana’antu masu fasahohin zamani suka janyo ya kai dalar Amurka biliyan 9.9, jimillar da ta kai kashi 33.2% na dukkan jarin waje da aka zuba wa kasar.
Kana idan an tantance asalin jarin, za a ga yawan kudin da kasashen Faransa, da Sifaniya, da Australiya, da Jamus, suka zuba a cikin kasuwannin Sin, ya karu da kashi 585.8% da 399.3% da 144.5% da kuma 19.8%, bisa na makamancin lokacin bara. (Bello Wang)